Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

00:00
00:00

Résumé de l'épisode

Fadar shugaban Najeriya, ta musanta alƙalumma da ke cewa bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta a cikin shekaru uku, ya kai Naira tiriliyan 120, inda ta bayyana ikirarin da ke cewa shugabanni 16 da aka yi cikin shekaru 63 da suka gabata, duka-duka bashin da suka ciwo bai zarta Naira trililyan 46, ba wani abu ba ne face farfagandar ƴan adawa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri......

Épisodes

781-

Fadar shugaban Najeriya ta magantu kan zargin ciyo bashin Naira triliyan 120

Fadar shugaban Najeriya, ta musanta alƙalumma da ke cewa bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta a cikin shekaru uku, ya kai Naira tiriliyan 120, inda ta bayyana ikirarin da ke cewa shugabanni 16 da aka yi cikin shekaru 63 da suka gabata, duka-duka bashin da suka ciwo bai zarta Naira trililyan 46, ba wani abu ba ne face farfagandar ƴan adawa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri......

09 nov. 2026
780-

Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda ƴan adawa ke cigaba da yaƙin neman zaɓe duk da ƙalubale

A Najeriya yayin da ake ci gaba da yaƙin neman zaɓen gamma-gari da za a yi cikin shekara mai zuwa, ƴan adawa sun yi zagin cewa ana hana su samun damar isa ga filayen da suka dace don gudanar da tarukan gangami, da rashin samun damar wallafa manufofinsu a allunan tallace-tallace da kuma rashin ba su cikakkiyar kariya ta tsaro a wasu jihohin ƙasar. Wannan shine maudu'in da muka baiwa mai sauraro damar tofa albarkacin bakinsa a kai. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Ɗan Bauchi.

05 nov. 2026
779-

Ra'ayoyi kan gargaɗin IMF cewa kada a kuskura a dawo da tallafin mai a Najeriya

Yayin da wasu daga cikin ƴantakarar neman shugabancin Najeriya ke bayyana yiyuwar sake dawo da tsarin biyan tallafin man fetur matukar suka yi nasarar lashe zaɓen shekara mai zuwa, a nasa ɓangare Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa ka da a kuskura a dawo da wannan tallafi. IMF ya bayyana cewa duk wani yunkurin sake dawo da tallafin, zai kasance mummunan koma-baya a maimakon cigaba ga Najeriya. Shin me ye ra’ayoyinku a game da wannan kashedi da ya fito daga Asusun IMF zuwa ga ƴansiyasar Najeriya? Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

15 oct. 2026
778-

Ra'ayoyi: Cikar Najeriya shekaru 10 ba tare da zartas da hukuncin kisa ba

A Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.

13 oct. 2026
777-

Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...

12 oct. 2026